Japan: Shekaru biyar da bala′in Tsunami | Labarai | DW | 11.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Japan: Shekaru biyar da bala'in Tsunami

Al'ummar Japan na gudanar da bikin cika shekaru biyar da afkuwar bala'in girgizar kasa da bala'in tsunami wanda ya hallaka mutane masu tarin yawa a kasar.

Tunawa da bala'in Tsunami a Japan

Tunawa da bala'in Tsunami a Japan

Yayin bikin a birnin Rikuzentakata an yi shuru na tsahon minti guda domin tunawa da mutane 18,000 din da suka rasa rayukansu yayin bala'in na Tsunami da ya afku a ranar 11 ga watan Maris na shekara ta 2011.

A ranar biyar ga watan Satumba na bara ne dai aka amince da komawar al'ummar birnin Naraha zuwa gidajensu, a matsayin birni na farko daga cikin bakwai da aka kwashe al'ummominsu sakamakon hadarin makamashin nukiliyar na Tsunami, sai dai watanni shida ke nan har kawo yanzu mazauna birnin 440 daga cikin 7,400 da aka kwashe a baya ne kacal suka koma.