Janye wata shari′ar cin hanci a Turkiya | Labarai | DW | 16.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Janye wata shari'ar cin hanci a Turkiya

Mai gabatar da kara a Turkiya ya janye duk wasu caje-caje da ake wa wasu manyan jami'ai a gwamnatin kasar kan wasu ayyuka masu nasaba da cin hanci da rashawa .

Wannan mataki ya shafi dukkanin mutane 53 da aka kama a shekarar bara ciki kuwa har da 'ya'yan tsaffin ministoci kamar yadda kamfanin dillancin labaran Dogan ya bada rahoto.

Binciken ayyukan cin hanci da rashawa ya sanya ministoci hudu sun sauka daga mukaminsu a wani abu da ya girgiza gwamnatin kasar ta Turkiya.

A Lahadin da ta gabata 'yan sanda sun cafke mutane 28 ciki kuwa har da 'yan jarida da ake alakanta su da Fetullah Gulen malamin nan da ke zama a Amirka wanda suka shiga takun saka da Recep Tayyip Erdogan saboda wasu batutuwa da suka hadar da bankada ayyukan cin hanci da rashawar .

Wannan kamen 'yan jarida dai ya jawo sukan kasar ta Turkiya daga kasashe irinsu Amirka da kasashen Kungiyar EU, kungiyar da kasar ta Turkiya ta dade tana marmarin shiga.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Muhammad Auwal Balarabe