An yi bikin tunawa da zagayowar ranar da aka 'yantar da sansanin gwale-gwale na 'yan Nazi a Buchenwald, inda mutane 56,000 suka mutu a lokacin yakin duniya na biyu.
A albarkacin zagayowar ranar tunawa da 'yantar da sansanin gwale-gwale Shugaban Jamus Frank-Walter Steinmeier, ya ce ya zama tilas Jamusawa su san cikakken tarihin tasa'ar da ta auku a sansanin na 'yan Nazi.
Shugaba Steinmeier a yayin jawabinsa na wannan shekarar ya ce duk wanda ya manta abinda ya faru, to babu makawa zai iya manta da abinda zai iya wakana a gaba.
Akalla mutum 56,000 ne suka mutu a yayin da sojojin Amirka suka kwace sansanin na Buchenwald daga hannun 'yan Nazi shekaru 76 da suka gabata a lokacin yakin duniya na biyu.