Jamus ta daura aniyar farfado da arzikinta | Labarai | DW | 02.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus ta daura aniyar farfado da arzikinta

A wani yunkuri na daidaita tattalin arzikin kasar, ministocin gwamnatin Jamus za su gudanar da taro da nufin kawo karshen kiki-kaka dangane da tallafin da gwamnatin kasar ta ware domin tallafawa masana'antun kasar.

Biyo bayan ta'annatin da annobar Corona ta yi wa tattalin arzikin kasashe a fadin duniya, Jamus ta lashi takobin farfado da tattalin arzikinta.

Babban batun da ake gani ka iya mamaye tattaunawar da ministocin kasar suka shirya shi ne batun kamfanonin kera motoci da ke kan gaba wajen bai wa al'umma aiki a kasar, wanda mai magana da yawun jam'iyyar SPD ya ce zai yi matukar wuya a samu matsaya a wannan ranar.

Takaddamar da ta barke tsakanin bangaren jam'iyyar masu ra'ayin mazan jiya ta Angela Markel da ke da ra'ayin rage haraji da kuma sassautawa 'yan kasuwa da kuma jam'iyyar 'yan gaba dai-gaba dai ta SPD da ke ganin a damkawa kowa tallafinsa a hannunsa shi ne mafi a'ala.