Jamus: Merkel ba ta yi da-nasani da shigowar 'yan gudun hijira ba | Labarai | DW | 28.08.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Merkel ba ta yi da-nasani da shigowar 'yan gudun hijira ba

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce idan da za ta sake samun dama za ta sake maimaita budewa 'yan gudun hijira kofa su shigo Jamus.

Merkel ta ce ba ta yi nadamar budewa 'yan gudun hijira kofar shigowa Jamus a shekara ta 2015 ba. Merkel ta yi wannan karin haske ne yayin wani taron 'yan jarida na lokacin bazara da ta saba yi shekara-shekara. 

Shugabar ta ce idan da za ta sake samun dama za ta sake maimaita hakan. Ta kuma ce har yanzu tana da ra'ayin idan mutane sun zo iyakar Jamus da Ostriya ko iyakar Hangari da Ostriya a rinka kula da su a tamkar mutane. 

Wannan ra'ayin nata dai ya janyo mata farin jini a kasashen duniya. Sai dai a nan Jamus masu kyamar baki sun sha gwasale ta.