1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Markus Söder ya amince da shan kaye

Mouhamadou Awal Balarabe
April 20, 2021

Shugaban jam'iyyar CSU Markus Soeder ya yarda da shan kaye a zaben fidda da dan takarar shugabancin gwamnatin Jamus daga bangaren masu ra'ayin mazan juya a zaben watan Satumba mai zuwa.

https://p.dw.com/p/3sHDR
Deutschland Markus Söder
Hoto: Peter Kneffel/REUTERS

Gwamnan jihar Bavaria da ke kudancin Jamus Markus Soeder ya amince da shan kaye a fafatawar da ya yi da shugaban jam'iyyar CDU Armin Laschet, don neman jagorantar kawancen masu ra'ayin rikau a zaben kasa baki daya da zai gudana a watan Satumba.

Soeder ya yanke shawarar mika kai ne bayan gwagwarmayar neman goyon baya ta mako guda, inda daga bisani manyan mambobin jam'iiyyar CDU suka goyi bayan Laschet cikin dare a matsayin dan takarar kawancen CDU da abokiyar tafiyarta ta CSU.

Sai dai Armin Laschet na fuskantar kalubale daga magoya bayan CDU da ke juya wa jam'iyyar baya sakamakon zargin gwamnatin Angela Merkel da rashin magance annobar COVID-19 da ke dada yaduwa a Jamus.

Tuni dai shugabar gwamnati Angela Merkel, wacce ta yi wa'adi hudu na mulki a jere ta taya Laschet murnar zama dan takara.