Jamus ba ta razana da matakan Girka ba | Siyasa | DW | 30.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus ba ta razana da matakan Girka ba

Tun bayan da jam'iyyar Syriza ta lashe zaben kasar Girka, sabon Firaminista Alexis Tsipras ya fara mayar da hannun agogo baya ga yarjejeniyar tsimin kudi da kasashen Turai suka cimma

Sai dai cibiyoyin tattalin arzikin Jamus sun ce wannan mataki bai razana su ba. Tun a taron farko na majalisar ministocinsa sabon Firaministan na Girka Alexis Tsipras ya sanar da dakatar da aikin sayar da ma'aikatun gwamnati ga 'yan kasuwa masu zaman kansu da ke zama wani bangare na yarjejeniyar sauye-sauyen tattalin arziki da Girka ta cimma da masu ba ta bashi na kasa da kasa. Sai dai Alexander Schumann masanin tattalin arziki na cibiyar masana'antu ta Jamus ya ce kamfanonin Jamus ba su ji tsoron wannan mataki na Tsipras ya dauka ba.

Girkan bata da karfi na azo a gani

"Karfin Girka a matsayin wani yankin zuba jari da samar da kayayyaki ko wurin tura kayayyaki daga Jamus ko bi a shigo da kaya Jamus, bai da wani muhimmanci. Kuma idan matakin sayar da kamfanonin kasa ga 'yan kasuwa bai yi wa Tsipras ba yana da 'yancin dakatar da shi, domin shi ne zababben shugaba. Yana neman wata hanya ta daban."

Taron ministocin kudi na EU

Taron ministocin kudi na EU

Shi ma Nicolaus Heinen masanin harkokin nahiyar Turai a bankin Deutsche Bank na mai ra'ayin cewa sauyin shugabancin a Girka ba zai yi wani tasir na a zo a gani ga tattalin arzikin Jamus ba domin kimanin kasa da kaso daya cikin 100 na kayayyakin da Jamus ke sayarwa a ketare ne yake zuwa Girka. Sannan babban bankin Tarayyar Jamus ya ce jarin kasa da kaso uku cikin 100 kasar ta zuba a Girka a shekarar 2012.

To sai dai kamfanin Fraport da ke tafiyar da filin jirgin saman birnin Frankfurt zai iya shiga wani hali sakamakon sauyin shugabancin a Girka. Kimanin watanni biyu da suka wuce kamfanin ya karbi kwangilar kula da filayen jiragen sama 14 a Girka a kan kudi sama da Euro miliyan dubu daya. A wannan shekara za a kammala kulla yarjejeniyar ta tsawon shekaru 40.

Girka ba za ta lamunci matakn tsuke aljihu ba

Masanin tattalin arziki

Masanin tattalin arziki

Sabon Firaministan na Girka ya ce kasarsa za ta ci gaba da zama cikin kasashe masu amfani da kudin Euro wato Eurozone amma ba zai mutunta abinda ya kira tilasta wa kasarsa daukar matakan tsuke bakin aljihu ba. Ahmet Cetinkaya na cibiyar Germany Trade & Invest ya yi karin haske.

"Tsipras ya nuna cewa ya gamsu da abubuwan da ke faruwa a kasashen Eurozone da ma kungiyar EU kanta. Kuma EU din za ta san irin dabarun da za ta tinkari Girka da su, kana za ta yi kokarin sakarwa Girka mara."

Sabon Firaministan na Girka dai ya zame wa Tarayyar Turai wani kadangaren bakin tulu da dole ta yi masa dan sassauci amma ba yadda wasu kasashe za su bi sahunsa ba.