Jamus: An zargi wani da zama dan Boko Haram | Labarai | DW | 26.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: An zargi wani da zama dan Boko Haram

Masu shigar da kara a Jamus sun sanar da kama wani Amaechi Fred O. mutumin da ake zargin da zama daya daga cikin mayakan Boko Haram da ke tada kayar baya a Najeriya.

Mutumin dan shekaru 27 ya shiga hannun jami'an tsaro ne a ranar Larabar da ta gabata a yankin Bavaria, bincike ya nuna cewa ya na daya daga cikin mayakan kungiyar da suka taba kai hari a wata makaranta da wani kauye dama yin garkuwa da mata a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Bisa ga bayanan da aka bada, Amaechi Fred ya zama mamba na kungiyar a shekarar 2013 ya kuma amince da hannu a wasu hare-hare hudu da mayakan suka kaddamar kan farraren hula a tsawon shekara guda da ya yi a karkashin kungiyar. An shigar da kara don soma gudanar da shari'a kan mutumin.