Jam′iyyun Amirka na zaben fidda gwani | Labarai | DW | 02.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyun Amirka na zaben fidda gwani

Ana dab da kammala kirga kuri'u a zaben fitar da gwani na 'yan takaran shugaban kasa da ya gudana a jihohi fiye da 10 na Amirka.

Manyan jam'iyyun siyasa na kasar ta Amirka wato Republican da Democrat, ne dai ke gudanar da zabubbukan na fida da gwani. A yanzu haka ana dab da kammala kidaya kuri'u a zaben 'Super Tuesday' da aka gudanar a wannan Talata daya ga watan Maris din da muke ciki. A jam'iyyar Republican Donald Trump ke kan gaba inda ya kama hanyar lashe jihohi 7, Ted Cruz ya samu jihohi biyu yayin da Marco Rubio ke da jiha 1, kana ana dakon sauran jihohin biyu. A bangaren jam'iyyar Democrat Hillary Clinton tana kan gaba a jihohi 7, yayin da Bernie Sanders yake kan gaba a jihohi 4.

Zaben na wannan Talata da ta gabata yana da muhimmanci kasancewar rana ce da ake zaben wakilai masu yawa fiye da kowace rana da ake zaben fitar da gwanin domin tantance 'yan takara biyu da za su fafata a zaben kasa baki daya na ranar takwas ga watan Nowamba mai zuwa. A wadannan zabubbuka ne dai za a gane wanda ka iya gadar kujerar mulki daga hannun Shugaba Barack Obama.

Yanzu haka an yi zaben fitar da gwanin a jihohi 15 saura 35, domin kasar ta Amirka tana da jihohi 50.