Jam’iyyun adawa a ƙasar Cadi sun yi watsi da sakamakon zaɓen ƙasar da aka buga. | Labarai | DW | 15.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam’iyyun adawa a ƙasar Cadi sun yi watsi da sakamakon zaɓen ƙasar da aka buga.

Jam’iyyun adawan ƙasar Cadi, sun yi watsi da sakamakon zaɓen da aka buga jiya, wanda ya bai wa shugaba Idris Deby rinjayi da kuma damar ci gaba da mulki har tsawon shekaru 5 masu zuwa, a wa’adi na 3.

Bisa sakamakon da hukumar zaɓen ƙasar ta buga jiya a birnin N’djamena dai, shugaba Deby ne ya lashe zaɓen, da samun kashi 77 da ɗigo 5 cikin ɗari na ƙuri’un da aka ka da. Su ko ’yan adawan, suna watsi da alƙaluman ne da bayyana cewa, yawan waɗanda suka ka da ƙuri’unsu a zaɓen takamaimai, bai kai adadin da hukumar ke dogaro a kansa ba.

A cikin wata fira da ya yi da kafar yaɗa labaran Reuters, shugaban rukunin CPDC, wanda ya haɗe jam’iyyun adawan, Lol Mahamat Choua, ya ce an tabka ɗanyen maguɗi a zaɓen. Sabili da haka ne suka ƙi amincewa da sakamakon.

Hukumar zaɓen ƙasar Cadin, mai zaman kanta, ta ce kashi 61 cikin ɗari na jama’a ne suka ka da ƙuri’un. Amma jami’an diplomasiyyan ƙasashen yamma, da kuma maneman labarai, sun ce yawan waɗanda suka ka da ƙuri’n bai kai haka ba.