Jam′iyyar PP ta sha kaye a zaben Spain | Labarai | DW | 21.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar PP ta sha kaye a zaben Spain

'Yan siyasa a kasar Spain sun fara shiri na girka sabuwar gwamnati bayan da jam'iyya Popular Party da ke mulki ta rasa rinjayen da ta ke da shi a majalisar dokoki.

Shugaban jam'iyyar Podemus Pablo Iglesias

Shugaban jam'iyyar Podemus Pablo Iglesias

Sakamakon da ya fita dai a zaben na jiya Lahadi ya nuna cewar jam'iyyar PP din ta sha kan sauran jam'iyyu a yawan kujerun da ta samu majalisar dokokin kasar sai dai hakan bai isheta ta iya jagorantar majalisar ba.

Jam'iyyar Socialist da ta Podemus da wasu kananan jam'iyyu a karon farko sun taka rawa ta a zo a gani a zaben, lamarin da ake ganin zai sauya alkiblar siyasar kasar ta Spaniya.

Pablo Iglesias da ke jagorantar jam'iyyar ta Podemus ya ce su na cike da farin ciki kasancewar babakeren da wasu jam'iyyu biyu suka yi ya kawo karshe kana za a bude wani sabon babi a fagen siyasar Spain.