Jam′iyyar PP ta lashe zabe a Spain | Labarai | DW | 27.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar PP ta lashe zabe a Spain

A Spain jam'iyyar PP ta masu ra'ayin mazan jiya, ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar da kujeru 137

Jam'iyyar Firaminista Mariano Rajoy PP ta masu ra'ayin mazan jiya ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a kasar Spain, inda ta samu kujeru 137 a yayin da jam'iyyar 'yan gurguzu ta samu kujeru 85, kana kawancan jam'iyyun Unidos Pademos ya tashi da kujeru 71. Sai dai kuma duk da haka jam'iyyar Firaminista Rajoy ba ta samu cikakken rinjaye na kujeru 176 daga cikin 350 da ta ke bukata domin kafa gwamnati ita kadai ba, koda yake Firmanista Rajoy ya ce lokaci ya yi da ya kamata a ba shi damar kafa gwamnati yana mai cewa:

"Muna bukatar samun 'yancin kafa gwamnati domin mun lashe zaben kuma daga yanzu burinmu shi ne, jagorancin al'umma baki daya wadanda suka zabe mu dama wadanda ba su zabe mu ba."

Yanzu haka dai jam'iyyar Ciudadanos wacce ta zo a matsayin ta hudu da kujeru 32 ta ce a shirye ta ke ta kulla kawance da jam'iyyar Firaministan ta PP, ko da yake ko sun kulla kawancan ba zai ba su damar samu cikakken rinjaye a majalisar kasar ba da zai ba su damar kafa gwamnati.