Jam′iyyar MPLA ta lashe zaben Angola | Siyasa | DW | 24.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jam'iyyar MPLA ta lashe zaben Angola

Jam'iyya mai mulki a kasar Angola ta MPLA ta yi nasara a zaben 'yan majalisar dokokin da ya gudana a ranar Labara a kaf fadin kasar, inda ta samu kashi 64 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.

Hukumar zaben kasar ce ta sanar da sakamakon a wannan Alhamis din, wanda hakan ke nuni da cewa dan takarar jam'iyyar mai mulki Joao Lourenço mai shekaru 60 da haihuwa ne zai gaji shugaban kasar mai barin gado José Eduardo dos Santos wanda ya mulki kasar tsawon shekaru 38.

Tsohuwar kungiyar 'yan tawayen kasar da ta rikide ta koma jam'iyya wato UNITA, ita kuma ta samu kashi 24.04 cikin 100 yayin da jam'iyyar Casa-CE ita kuma ta samu kashi 8.56 cikin 100 a cewar mai magana da yawun hukumar zaben kasar ta Angola Julia Ferreira yayin wani taron manema labarai.

A shekara ta 1975 ne dai kasar ta Angola ta kwaci mulkin kanta daga hannun turawan mulkin mallaka na kasar Portugal kuma jam'iyyar MPLA da ke mulki tsawon wannan lokaci a kasar, ta samu babban rinjayen da ake bukata na kujeru 220 a majalisa, wanda hakan zai bata damar tsayar da shugaban kasa.