Jam′iyyar LDP a Japan ta samu rinjaye | Labarai | DW | 10.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar LDP a Japan ta samu rinjaye

Wani hasashe da wasu manyan gidajen talabijan na Japan suka bayyana bayan kammala zaben 'yan majalisun dokoki, ya nuna cewar jam'yyar LDP da kawayenta za su samu nasara.

Bayanan hasashen sun ce jam'iyyar Liberal Democratic Party LDP a takaice, ta masu ra'ayin rikau da kawarta ta Komeito sun samu kujeru 67 daga cikin kujeru 76 na 'yan majalisun. Jam'iyyar ta LDP wacce ke mulkin a Japan tun daga shekara ta 1955 ba tsaiko, ta kalubalanci jam'iyyar masu tsatsauran ra'ayi wacce karfinta ya ragu sosai a Japan, kuma idan nasarar ta tabbata a karon farko za a yi wa kundin tsarin mulkin na Japan din kwaskorima domin kaddamar da wasu sauye-sauye a harkokin gudanar da mulki.