1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jam'iyya mai mulki ta lashe zaben 'yan majalisar dokoki

Ramatu Garba Baba
June 15, 2021

Jam'iyyar mai mulki ta FLN ta kasar Aljeriya ce ke sahun gaba a kuri'un da aka kidaya a zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.

https://p.dw.com/p/3uz9A
Algerien Präsidentschaftswahl
Hoto: picture-alliance/AP/D. Cole

Jam'iyyar FLN ta kasar Aljeriya ta lashe akasarin kujeru a zaben 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata. Hukumar zaben kasar ce ta sanar da hakan, sai dai duk da wannan nasarar, tana bukatar karin kuri'u kafin ta sami rinjaye a halin da ake ciki a kasar da ta sha fama da zanga-zangar neman sauyi.

Jam'iyyar ta FLN ta yi ma sauran fintinkau bayan da ta sami kujeru 105, Jam'iyyar Independent Candidates ta sami kujeru 78 a yayin da jam'iyyar MSP ta sami kujeru sittin da hudu. Ana bukatar kimanin samun kujeru 204 daga cikin 407 kafin jam'iyya ta sami rinjaye a majalisar kasar ta Aljeriya. Masana na ganin da wuya zaben 'yan majalisar dokoki, ya yi tasirin kawo canji a dimukuradiyyar kasar.