Jam´iyyar ANC na kokarin darewa izuwa gida biyu | Labarai | DW | 07.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam´iyyar ANC na kokarin darewa izuwa gida biyu

Fafutikar neman madafun iko na jam´iyyar ANC a Africa ta kudu a yanzu haka ya fara tsananta. Kwanaki kadan ya rage a fara zaben, tuni wakilai dubu 2 da dari 5 da zasu shiga zaben suka fara zaben share fage na dan takarar su. A yanzu haka dai ya tabbata a fili cewa za´ayi takarar ne, a tsakanin shugaba Thabo Mbeki da kuma tsohon mataimakin sa Mr Jacob Zuma. Ci gaba da fito na fiton shugabannin biyu dai, an bayyana cewa abune daka iya kawo darewar jam´iyyar ta ANC izuwa gida 2.Rahotanni dai sun shaidar da cewa manufar takarar Mr Mbeki, shine na kawo cikas ga takarar tsohon mataimakin na sa. Kundin tsarin mulkin na Africa ta kudu dai ya hanawa Mr Mbeki kara tsayawa takarar neman shugabancin kasar, bayan karewar wa´adin sa na biyu a shekara ta 2009. Bisa al´ada dai, duk mutumin da jam´iyyar ta ANC ta zaba a matsayin shugabanta, shi ya kann kasance dan takarar ta a zaben shugaban kasa.