1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka ta Kudu

Jam'iyyar ANC a Afirka ta Kudu ta kira babban gangami

May 25, 2024

Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu na wani gagarumin gangamin da ake ganin shi ne irinsa na karshe gabanin zaben kasa da za a gudanar a makon gobe.

https://p.dw.com/p/4gHTG
Hoto: picture-alliance/B. Curtis

Jam'iyyar shugaban kasar Cyril Ramaphosa ta kira magoya bayanta ne a manyan filayen wasa na yankin Soweto da ke a birnin johannesburg a kokarin nemo tagomashinta, domin cike gibin da ta samu a zaben da ya gabata.

Zaben da za a yi shi a ranar Larabar da ke tafe ana ganin zai iya kasancewa zaben da jam'iyyar jagoran dimukuradiyya da ya kawo karshen wariyar launin fata wato Nelson Mandela za ta rasa samun rinjaye a cikinsa.

Masu nazarin harkokin siyasa a Afirka ta Kudun na ganin daga cikin wadanda za su iya yi wa ANCn lahani har da jam'iyyar da tsohon shugaban kasa Jacob Zuma ya kafa a baya-bayan nan.