Har yanzu ana samun tsaikon kan sakamakon zaben Myanmar.
November 10, 2015Talla
Mai magana da yawun jam'iyyar League Democaratic Party Win Htein ya fadawa manema labarai a yau talatar nan cewar mai yuwane hukumar zaben Myanmar din na wata kunbiya-kunbiya ce ga batun sanar da sakamakon zaben.
Hukumar zaben Myanmar din dai tun ranar lahadin nan ce ta futar da wasu sakamakon zaben a inda sakamakon ke nuni da cewar Jam'iyyar League Democaratic party ce ke kan gaba dake a karkashin jagorancin Au San Syk.
kazalika Win yace yadda hukumar zaben take sakin sakamakon zaben kadan-kadan bai dace ba kamata yayi a bayyana sakamakon baki daya.