Masu mulki sun yi rinjaye a zaɓen Burundi
July 7, 2015Talla
Jam'iyyar da ke mulki a ƙasar Burundi ta shugaba Pierre Nkurunziza ta lashe mafi rinjayen kujerun majalisar ƙasar a zaɓen mai cike da ruɗani.Hakan ya bayyana ne a cikin wani sakamako da hukumar zaɓen ƙasar ta fitar a ranar Talatan nan.
Jam'iyyar ta CNDD-FFD ta shugaba Nkurunziza da ke neman tazarce a karo na uku a zaɓen ƙasar da ke tafe, ta samu nasarar lashe kujeru 77 daga cikin 100 na majalisar, a cewar hukumar zaɓen ƙasar.Wannan sakamako dai na zuwa ne duk da ƙauracewar da 'yan adawa suka yi a zaɓen da ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa hadi da Majalisar Ɗinkin Duniya suka ce bai cika sharuƊa ba na zama sahihi.