1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban jama'a sun yi zanga-zangar nuna adawa da gwamanti

Abdoulaye Mamane Amadou
March 11, 2019

Dubun dubatar jama'a sun yi zanga-zangar nuna adawa da matakin na kakaba wata dokar da ke hana jam'iyyun adawa shiga takara a zaben 'yan majalisun dokokin da ake shirin gudanarwa a watan gobe.

https://p.dw.com/p/3Eogn
NO FLASH Benin Cotonou Straße
Hoto: picture-alliance/dpa

A Jamhuriyar Benin yan adawa sun fito don kalubalantar dokar da ke hana jam'iyyun adawar  shiga takara a zaben 'yan majalisun dokokin kasar da ake shirin gudanarwa a ranar 28 ga watan Aprilu.

Kawancen jam'iyyun adawa ne dai ciki har da na tsohon shugaban kasar Thomas Yayi Boni da mai gogon bayan dan siyasar nan kuma hamshakin dan kasuwa  Sebastien Ajavon ne suka shirya gangamin, da ya tattara magoya baya akalla dubu 20 a kan titunan birnin Cotonou don cilastawa gwamnatin kasar soke dokar.

Yan adawar dai a baya sun kauracewa duk wata tattauanwa da shugaban kasar biyo bayan nuna bukatar hakan, suna masu cewa babu wata kwakwarar hujjar da za ta kai shugaban daukar wannan mataki.

Kawo yanzu jam'iyyun siyasa biyu kawai na bangaren masu mulki suka kai ga cika sharadin shiga takarar ta 'yan majalisa da ake shirin gudanara a karshen watan Aprilun wannan shekara.