1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuncin zaman kaso ga 'yan adawar Benin

December 14, 2021

Kotun Hukunta Laifukan Almundahana da Dukiyar Kasa da Ta'addanci a Jamhuriyar Benin, ta zartar da hukuncin daurin gidan yari ga wasu jiga-jigan 'yan adawar kasar.

https://p.dw.com/p/44GLt
Benin | Rückkehr von Kunstobjekten in Cotonou
Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice TalonHoto: Séraphin Zounyekpe

A farkon wannan wata na Disamaba da muke ciki ne dai, kotun ta yanke hukuncin da tuni ya haifar da cece-kuce a kasar. Hukuncin daurin gidan yarin na tsawon shekaru 10 a gidan kaso ne dai, kotun ta yanke wa Frédéric Joel Aivo kana ta yankewa Réckyatou Madougou hukuncin zaman gidan kaso na shekaru 20. Alkalan kotun mai Hukunta Laifukan Almundahana da Dukiyar Kasa da Ta'addanci ta Benin, sun kama jiga-jigan 'yan adawar ne da laifin aikata laifukan halasta kudaden haram da na ta'addanci. Duk da yake wannan ba shi ne karon farko da ake hasashen gwamnati na amfani da kotuna domin karya lagon 'yan adawa ba, wasu masanan doka irin mai shari'a Jacques Migan na ganin cewa hukuncin ba shi da wata nasaba da siyasa.

Benin | Präsidentschaftswahl 2021 | Transport der Wahlurnen
A shekara ta 2023 ne dai, al'ummar Jamhuriyar Benin za su gudanar da zabeHoto: Séraphin Zounyekpe/DW

Sai dai shi kuwa masanin siyasar kasar ta Benin Expédit Ologou na da ra'ayi mabambanci da lauyan mai zaman kansa kuma kwararre a fannin shara'a, domin kuwa a cewarsa kotun ce ma kacokam aka kafa domin amfani da ita wajen muzgunawa 'yan adawa da tauye duk wani da ake hasashen ka iya caccakar wasu manufofi da suka shafi tafiyar da harkokin mulki. Wannan hukunci dai na ci gaba da daukar hankula a kasashen duniya, yayin da kuma yake zuwa ne a yayin da kasar ta Jamhuriyar Benin ke shirin tunkarar zabukan 'yan majalisun dokoki a shekarar 2023 da ke tafe. Kasar dai na fama da rikici irin na siyasa, inda manyan jam'iyyun siyasa a Jamhuriyar ta Benin ke ci gaba da yin zama irin na doya da manja a tsakaninsu.