Jama′a sun kauracewa rumfunan zaben Masar | Labarai | DW | 22.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jama'a sun kauracewa rumfunan zaben Masar

Rukuni na biyu a zaben majalisar dokoki ya gudana amma 'yan kalilan suka fito, duk kuwa da baza jami'an tsaro a fadin kasar don gudun barkewar tarzuma

A kasar Masar wannan Lahdi 22.11.2015 aka gudanar da zaben rukuni na biyu na 'yan majalisar dokoki, domin samar da majalisar da za ta yi wa kasar doka. Sai dai a cewar masu aiko da rahotanni zaben rukunin na biyun kamar rukunin farko da aka yi, kusan 'yan kalilan mutane aka gani a rumfuna, bayan da mutanen suka kauracewa fita zabe. Dama dai tun a shekara ta 2012, sojoji suka rusa majalisar dokoki ta farko da jama'a suka zaba bisa tsarin demokradiya, bayan da suka shigar da kara a kotu. Duk da cewa rumfunan sun kasance wayam amma an baza tarin sojoji don gadin 'yan rumfunan zabe, ganin irin tarzuma da kasar ke fiskanta.