1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wakilin Amirka a Afganistan ya bar aiki

Abdul-raheem Hassan
October 19, 2021

Bayan murabus din wakilin Amirka na musamman a kasar Afganistan Zalmay Khalilzad, 'yan Afghanistan na cewa dama ba su gamsu da rawar da ya taka a kasar ba.

https://p.dw.com/p/41rc4
USA Sondergesandter für Afghanistan Zalmay Khalilzad
Hoto: Rod Lamkey/CNP/MediaPunch/imago images

Wasu daga cikin 'yan kasar Afganistan na zargin babban jami'in diflomasiyyar Washington da ya yi murabus a mastayin wanda ya taimakawa kungiyar Taliban samun nasarar kwace iko da gwamnati a farkon watan Agustan 2021.

Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta tabbatar da murabus din Khalilzad, sai dai da yake maida martani kan wannan mataki, tsohon babban jami'in leken asirin Afganistan Rahmatullah Nabil ya kwatanta Khalilzad a matsayin mutumin da ya jefa kasar Afganistan cikin bala'in da ba za su iya fita ba.