Jakadar Jamus a Yemen ta tsira da kyar | Labarai | DW | 07.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jakadar Jamus a Yemen ta tsira da kyar

Jami'in da ke kare lafiyar jakadar Jamus a Yemen ya rigamu gidan gaskiya a wani hari da aka kai musu a birnin San'a. Sai dai Jakadar Carola Müller-Holtkemper ta tsallake rijiya da baya.

An harbe wani ma'aikacin ofishin jakadan kasar Jamus har lahiya a birnin Sanaa na kasar Yemen a kusa da rukunin shaguna kusa da inda ofisoshin jakadanci suke. An yi imanin cewar wanda aka hallaka shi ne jami'in da ke kare lafiyar jakadiyar kasar ta Jamus a Yemen, Carola Mueller-Holtkemper.

Hukumomin Jamus sun kaddamar da bincike domin sanin hakikanin abin da ya faru, saboda akwai jita-jitar cewa maharan sun yi yunkurin garkuwa da jakadar ce. Amma haka ya ci tura saboda jakadar saboda ta tsallake rijiya da baya. Kwanaki kalilan da suka gabata ne ta fara aiki. Cikin tsakiyar watan Agusta saboda dalilan yiwuwar kai harin ta'addanci ya sa an rufe ofishin jakadancin na Jamus kafin daga bisani a sake budeshi.

Duk da sauyin gwamnati da aka samu, kasar ta Yemen ta na ci-gaba da fama da rikice-rikicen da ake dangantawa da kungiyar al-Qaeda.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe