Jagorar ′yan adawa a kasar Myanmar tace zata zarta mukamin shugaban kasa muddin jam′iyar ta ta samu rinjaye. | Labarai | DW | 05.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagorar 'yan adawa a kasar Myanmar tace zata zarta mukamin shugaban kasa muddin jam'iyar ta ta samu rinjaye.

Jagorar jam'iyyar adawa a kasar Myanmar Aung San Suu Kyi ta bayyana cewar mukamin ta zai zarta na shugaban kasa muddin suka sami nasara a zaben dake tafe na ranar 8 ga watan Nuwamba.

Wannan zaben dake tafe dai shine irin sa na farko tun lokacin da jagoran kasar ya karbe ragamar mulkin kasar a shekara ta 2011 bayan shafe kusan shekaru 50 kasar na karkashin jagororin mulkin soji.

A yayin da take fadawa manema labarai San Suu Kyi tace zata dara mukamin shugaban kasa muddin suka sami rinjaye a zaben kasar mai cike da tarishi.

A yan kwanakin nan dai jagorar yan adawar kasar Myanmar tasha suka daga bangarori da dama akan gaza tashi tsaye don ganin an kare tsirarun kabilu dake a yankin Rohingya na kasar.