Jagorar AfD ta raba gari da jam′iyyar | Siyasa | DW | 26.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jagorar AfD ta raba gari da jam'iyyar

Frauke Petry ta jam'iyyar (AfD) me kyamar baki ta yi hannun riga da jam'iyyar abin da ke zuwa kwanaki kalilan bayan nasarar da suka samu ta shiga majalisa.

Duk da cewar tun a zaben na 2013 jam'iyyar ta (AfD)  ba ta kai labari dangane da samun kason da zai bata damar shiga majalisar tarayya ba, ta samu nasar kutsa kai cikin majalisu a mataki na jihohin Jamus. Sai dai sabanin hasashen da aka yi gabanin zaben na ranar Lahadi, jam'iyyar mai akidar kyamar baki ta samu gagarumar nasara da har ya kaita ga zama ta uku mafi karfi a tsakanin jam'iyyun Jamus.

Shin wane kalubale 'yan majalisar dokoki na sauran jam'iyyun za su fuskanta daga jam'iyyar ta AfD? Thomas Mösch mai sharhi ne kan lamuran siyasar Jamus kuma shugaban sashin Hausa na DW, ya ce babban abin da zai zama kalubale ga sauran jam'iyyun shi ne yadda za su tunkari yadda jam'iyyar ke bayyana kyama ta baki kamar bakar fata ko Musulmi idan suka shiga majalisar ta Jamus.

Deutschland Bundestagswahl Frauke Petry verlässt die PK

Petry lokacin barin zaman 'yan AfD

Kin jinin baki na zaman daya daga cikin irin abubuwan da ake tunawa da zarar an yi magana game da jam'iyyar AfD da aka kafa shekaru hudu da suka gabata. AfD na son rufe iyakokin Turai da matsa bincike a iyakokin Jamus da kafa sansanoni a kasashen waje don tare 'yan gudun hijira, ga shirin mayar da duk wanda ya rasa mafakar siyasa inda ya fito, da tisa keyar mutane zuwa wajen kasar ta hanyar ma tallafa musu.

Jam'iyyar ta AfD na da mambobi dubu 27, kuma 'yan takarar jam'iyyar a wannan zaben majalisar tarayya da ya gudana a ranar Lahadi dai su ne Alexander Gauland da Alice Weidel. Shugabar jam'iyyar kuwa Frauke Petry bayan da ta samu kanta a majalisar sakamakon rawar da ta taka ta ma fice daga jam'iyyar baki daya inda za ta taka rawa a majalisa a matsayin 'yar majalisa mai cin gashin kanta.

 

Sauti da bidiyo akan labarin