Jagoran soja ya muzanta 'yan Rohingya
October 12, 2017Jagoran soja a Myanmar ya bayyana cewa Musulmai 'yan kabilar Rohingya ba 'yan asalin Myanmar ba ne, ya bayyana haka ne kuma a lokacin zantawa da jakadan Amirka. sai dai bai yi masa bayani ba dalla-dalla kan zargin sojansa da ake yi na cin zarafin wadannan al'umma marasa rinjaye a kasar. sai dai ya ce kafafan yada labarai na zarce makadi da rawa kan yadda suke zuzuta labarin.
Janar Min Aung Hlaing ya yi rubutu mai tsawon a kan shafinsa na Facebook wanda yake da muradin duniya ta gani inda a nan ne ya yi jawabi kan ganawar tasa da jakadan na Amirka Scot Marciel. Janar Min Aung Hlaing da ya bayyana 'yan Rohingya da "Bengali", sunan da basa so a bayyanasu da shi.
Ya ce Turawan mulkin mallaka na Birtaniya su ne kanwa uwar gami a rikicin kasar. Kalaman sojan dai da ke da karfin fada a ji a Myanmar sun nuna rashin tausayawa ga al'ummar da sama da mutane dubu 500 na su suka kauracewa jiharsu ta Rakhine da ke Arewaci.