Jagoran Facebook ya nemi afuwa | Labarai | DW | 22.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagoran Facebook ya nemi afuwa

Mark Zuckerberg ya ce wajibi ne ya dau matakan inganta manhajar don kare bayanan masu amfani da shafukan Facebook daga masu kutse.

Jagoran kamfanin sada zumunta na Facebook, ya nemi afuwar mutane akalla miliyan 50 kan yadda kamfanin Cambridge Analytica ta yi, wa masu amfani da shafukan kutsen bayan don cimma manufofi irin na siyasa.

Yayin wata hira da talabijin na CNN bayan bankado satar bayanan da kamfanin Cambridge Analytica ya yi, Zuckerberg ya ce tabbas an ha'inci jama'a. Tun dai bayan aukuwar lamarin, hannayen jarin kamfanin Facebook ya fadi da kashi Takwas cikin dari.