Jagoran adawa a Kenya ya yi zargin magudi | Labarai | DW | 02.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jagoran adawa a Kenya ya yi zargin magudi

Jagoran jam'iyyar adawa a Kenya Raila Odinga ya ce babu yadda za a yi jam'iyya mai ci ta sake lashe zaben shugabancin kasar sai dai ta hanyar magudi.

Jagoran jam'iyyar adawan kasar Kenya Raila Odinga, ya ce babu ta yadda za a yi jam'iyya mai ci ta sake lashe zaben shugabancin kasar sai dai ta hanyar magudi. Mr. Odinga ya fadi hakan ne a lokacin yakin neman zabe da ya kai shi a garin Susan da ke kusa da Nairobi babban birnin kasar.Madugun 'yan adawar ya na fafatawa da shugaba mai ci Uhuru Kenyatta a babban zaben shugabancin kasar da zai gudana a makon gobe.

Al'ummar kasar da dama na fargabar barkewar rikici makamancin wanda ya auku shekaru goma da suka gabata inda aka samu asarar rayukan mutane fiye da dubu guda.