Iyayen ′yan matan Chibok sun gana da Buhari | Labarai | DW | 14.01.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iyayen 'yan matan Chibok sun gana da Buhari

Daruruwan masu fafutukar ceto 'yan matan makarantar Chibok da aka fisani da Bringback Our Girls ne suka hau kan titunan birnin Abuja a Najeriya

Yan kungiyar ceto yan matan Chibok din dai sun hau kan titunan birnin Abuja domin nuna takaicin su a bisa rashin ceto matan daga hannun Boko Haram har yanzu.

Shugabar hada tauwagar tattakin zuwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, Oby Ezekwesili da ke zama tsohuwar minisatan ilimin Najeriyan ta yi nuni da cewar.

"Abin da shugaban kasa ya fada a jawabin sa ga manema labarai lokacin daya gana da su, na cewar basu da wasu sahihan bayanan a inda 'yan matan suke, gaskiya ne karara ya fada, kuma bai yi wata rufa-rufa ba".

Kazalika ta kara da cewar shugaba Buhari ya nuna cewar a yanzu haka basu da bayanan sirri inda matan suke, kamar yadda muke matukar san ganin su. Tun dai a watan Aprilun shekara ta 2014, 'yan kungiyar Boko Haram suka sace yaran susukimanin 276 a makarantar Chibok da ke jihar Born.