Iyayen ′yan matan Chibok na kara zura ido bayan da wasu suka kubuta | Siyasa | DW | 07.07.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Iyayen 'yan matan Chibok na kara zura ido bayan da wasu suka kubuta

Yadda 'yan matan ke kubuta da zarar sun sami sarari, duk da irin muggan makaman da ake cewa masu tsare da su na da shi, na sanya alamar tambaya kan yunkurin ceto sun da gwamnati ke ikirarin yi

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya na nuni da cewa wasu daga cikin matan da aka sace a jihar a watan Yunin da ya gabata sun samu nasarar tserewa daga wadanda ke tsare da su.

Daya daga cikin 'yan kato da gora dake taimakawa wajen yakar 'yan Boko haram a jihar ta Borno Abbas Gava ya bayyana cewa wani abokin aikinsa ya shaida masa cewa 63 daga cikin matan sun koma gida tun ranar Jumma'ar da ta gabata. Shi ma wani babban jami'in tsaro a jihar ta Borno da ya bukaci a boye sunansa ya tabbatar da nasarar tserwa da zuwa gida da matan suka samu.

Kungiyar kato da gora na taimako wajen tabbatar da tsaro

Abbas Gava na kungiyar kato da gora a jihar ta Borno ya shaidawa manema labarai cewa matan sun samu nasarar tserewa ne a yayin da masu tsaronsu suka fita fada. Wani masani kan al'amuran tsaro a Tarayyar ta Najeriya Dr. Bawa Abdullahi Wase ya ce gwamnatin Najeriya bata da niyyar ceto su shi ya sanya ma da sun samu dama suke tseratar da rayuwarsu da kansu.

Batun Boko Haram ko kuma tabarbarewar al'amuran tsaro a tarayar ta Najeriya dai ya zamo wani babban taashin hankali da kalubale dake fuskantar kasar da ta yui ikirarin zamowa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka kuma adai dai lokacin da zabukan da za a gudanar a kasar a shekara ta 2015 ke kara karatowa domin kuwa ko da a ranar Jumma'ar da ta gabatanma ssai da aka yi musayar wuta tsakanin 'yan ta'addan da jami'an tssaro a garin Damboa na jihar Borno inda rahotanni ke cewa akallah sama da 'yan ta'addan 50 ne suka sheka barzahu yayin wannan fafatawar.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba

Sauti da bidiyo akan labarin