Italiya guda ce daga cikin kasashen da ke Kungiyar Tarayyar Turai ta EU. Kasar na da yawan mutane kimanin miliyan 60 kana ita ce ta uku mafi karfin tattalin arziki a kungiyar EU.
Kasar na daga cikin kasashen da ke da karfin fada a ji a Turai. Italiya ta yi iyaka da kasashen da suka hada da Faransa da Switzerland da Austireliya da Vatican City. A halin yanzu birnin Rome shi ne baban birninta.