An sa dokar hana zanga-zanga a Italiya gabanin ziyarar Erdogan a Vatikan | Labarai | DW | 05.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An sa dokar hana zanga-zanga a Italiya gabanin ziyarar Erdogan a Vatikan

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai gana da shugaban darikar Katolika Paparoma Francis a Vatikan, lamarin da ya sanya mahukuntan Italiya haramta duk wata zanga-zanga har tsawon awanni 24.

Ziyarar irinta ta farko a cikiin shekaru 59, a halin yanzu an baza jami'an tsaro da yawansu ya kai 3,500 a fadin birnin Rome.

Sai dai a nasu bangaren 'yan kungiyar Kurdawa mazauna Italiya kimanin mutane 200 sun dauki aniyar yin wani zaman dirshan a wannan Litinin a fadar Vatikan don nuna kin jininsu da abin da ke faruwa a kan 'yan uwansu da ke Siriya.

Ana sa ran Paparoma Francis zai tabo batun kai harin yankin Afrin a ganawar da za su yi da Shugaba Erdogan.