Italiya ta yi barazanar hana jiragen bakin haure yada zango a kasar | Labarai | DW | 29.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya ta yi barazanar hana jiragen bakin haure yada zango a kasar

Jakadan kasar ta Italiya zuwa Kungiyar EU Maurizio Massari, ya ce abu ne da ba za a lamunta ba dukkanin jiragen aikin jinkai su yada zango a gabar teku na yankin Italiya.

Kasar Italiya ta yi barazanar hana jiragen kasashen waje da ke aikin agaji ga mutanen da aka ceto daga tekun Bahar Rum zuwa yankin kasarta, bayan da ta ce ana samun sabbin adadi na masu kwarara a hanyarsu ta zuwa Turai.

Jakadan kasar ta Italiya zuwa Kungiyar EU Maurizio Massari, ya ce abu ne da ba za a lamunta ba dukkanin jiragen aikin jinkai su yada zango a gabar teku na yankin Italiya.

Fiye da bakin haure 10,000 ne suka isa Italiya a 'yan kwanakin nan, abin da ya sanya shekaru uku da suka gabata aka samu 'yan gudun hijirar 500,000. Ko da yake wasu jami'an sojan na Italiya da ke aikin kula da gabar teku su suka ceto wasu sun isa yankin kasar a jirage na kungiyoyi masu zaman kansu dauke da tutocin kasashen waje.