Italiya ta juya baya ga ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 15.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya ta juya baya ga 'yan gudun hijira

Kungiyar agaji ta Sea-Watch ta kasar Jamus ta bayyana cewa ta ceto bakin haure 65 daga teku bayan sun baro gabar teku daga Libiya a wannan rana ta Laraba,

Ministan harkokin cikin gidan Italiya me ra'ayin rikau Matteo Salvini ya sha alwashi na cewa ba zai bari ba a kawo 'yan gudun hijirar zuwa gabar teku a Italiya.

An dai kwaso 'yan gudun hijirar a tsakiyar ruwan kasa da kasa da tazarar kilomita 55 arewa daga tashar gabar teku ta Zuwara, kuma a cewar mai magana da yawun kungiyar ta Sea-Watch dukkanin mutanen da aka ceto suna tare da su.
Salvini dai da ke zama mai ra'ayin rikau kan adawa da shigowar bakin ya ce ta hanyar daukar mataki mai tsauri ne kawai zai sa bakin hauren su rika shayin yin kasada ta ratso teku a kokari na kai wa Turai daga Afirka.

Ya dai sha wannan alwashi na nuna adawa da zuwan bakin adaidai lokacin da 'yan takara ke kara zawarcin kuri'un masu zabe, a zaben 'yan majalisar Tarayyar Turai a ranar 26 ga watan nan na Mayu a Italiyan.