Italiya ta ceto ′yan gudun hijirar Afrika a tsibirin Sicily | Labarai | DW | 07.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Italiya ta ceto 'yan gudun hijirar Afrika a tsibirin Sicily

Mai magana da yawun dakarun tsaron gabar ruwan Kasar Italiya ta ce sun sami nasarar ceto kimanin sama da 'yan gudun hijirar Afirka dari 300 daga cikin wani takuraren jirgi.

Jirgin dai ya futo ne daga kasar Misira dauke da 'yan Afirka a inda ya yada zango a tsibirin Sicily na Italiya.Mutanen dai da ke tserewa yake-yake da matsalar yunwa a Afirka da Gabas ta Tsakiya na ci gaba da nausawa gabar ruwan Italiyan shekaru da dama da suka gabata a yayin da akasari suke amfani da Libya a inda suke biyan masu fataucin su domin samar musu hanya shiga Turai.

Mai magana a yawun Gabar ruwan Italiyan ta ce 'yan gudun hijirar da suka tsare sun hada da 'yan Kasashen Syriya da Misira da Somalia da Eritiriya da Habasha gami da 'yan Sudan.