1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta soki manyan kasashen Duniya

Zulaiha Abubakar
May 16, 2018

Ministan tsaron Israila Avigdor Lieberman ya ja hankalin rundunar sojin kasar akan su yi watsi da kiraye-kirayen da manyan kasashen duniya suke yi akan matakin da suke dauka.

https://p.dw.com/p/2xqcE
Avigdor Lieberman Ministan tsaron kasar Isra'ila
Avigdor Lieberman Ministan tsaron kasar Isra'ilaHoto: Reuters

Wannan jan hankali da Ministan yayi ya biyo bayan wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tweeter inda ya bayyana kasashen da suke sukar matakin da Isra'ilan ke dauka akan Falasdinawa da cewa Munafukai ne. 

A nata bangaren Kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta bayyana cewar ya zuwa yanzu akalla Falasdinawa fiye da sittin ne suka rasa rayukan su yayin arangama tsakanin su da Sojojin Isra'ila a ranar litinin din da ta gabata.

A wani cigaban kuma shugaban kasar Rasha Vlamir Putin da takwaransa na kasar Turkiyya sun yi Allah wadai da harin da Isra'ila ke cigaba da kai wa yankin Gaza.