1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hamas ta sanar da tsagaita wuta a Gaza

Ramatu Garba Baba
May 30, 2018

Daya daga cikin jagororin kungiyar Falisdinawa ta Hamas ya ce sun cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Isra'ila a wannan Laraba bayan wani zama da aka yi a tsakanin wakilan bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/2yZd5
Gaza Israel Konflikt Jerusalem US Botschaft
Hoto: Reuters/I. Abu Mustafa

Khalil al-Hayya a wata sanarwar da ya fitar ya ce wakilai da masu shiga tsakani sun kwashi sa'oi suna zaman tattaunawa inda daga bisani suka yi nasarar shawo kan bagarorin tare da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wutar a zirin Gaza, ya kara da cewa su a nasu bangaren a shirye suke su mutunta ka'idojin da aka gindaya a karkashin yarjejeniyar muddun Isra'ila za ta bayar da hadin kan da ake bukata.

Jim kadan da wannan sanarwar,  Isra'ila ta bakin ministan kula da harkokin leken asirinta ta mayar da martani inda ta musanta wannan labari. Tarzomar baya bayan nan a yankin na Gaza kan bude ofishin jakadancin Amirka ya kasance mafi muni tun na yakin 2014. Falisdinawa kusan sittin ne suka halaka wasu fiye da dubu biyu kuma suka sami rauni.