1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta sake kai hari zirin Gaza

Abdul-raheem Hassan
June 16, 2021

Sojojin Isra'ila sun harba rokoki zuwa Gaza a mastayin ramuwar gayya, bayan tashin gobara a yankunanta da dama sakamakon ababen fashewa da kungiyar Hamas ta harba.

https://p.dw.com/p/3v0Ma
Erneute Angriffe in Gaza City
Hoto: Mahmud Hams/AFP

A karon farko tun bayan kawo karshen rikicin kwanki 11 a zirin Gaza, wanda ya yi sanadiyar mutuwar Faladsinawa sama da 200, Isra'ila ta kaddamar da hare-haren ramuwar gayya zuwa zirin gaza, bayan da kungiyar Hamas ta harba balam-balam masu fashewa da suka haddasa gobara a wasu yankunan Isra'ilar.

Matakin ya biyo bayan wani tattaki da Yahudawa masi kishin kasa su ka yi a gabashin birnin Qudus a ranar Talata, wanda ya haifar da kakkausar suka daga bangaren Hamas wacce ke iko da Gaza a hukumance.