Isra'ila ta kai hari Lebanon bayan yin sulhu
June 20, 2026
Talla
Kamfanin dillancin labarai na Lebanon ya ruwaito cewa, Isra'ila ta yi amfani da jiragen yaki da kuma jirage marasa matuka wajen kai farmakin yankin Nabatieh a cikin daren, wanda ya yi sanadin lalacewar rukunin gidajen jama'a.
Karin bayani: Tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Lebanon ta fara aiki
A ranar Juma'a ce Isra'ila da Hezbollah suka amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta biyo bayan wani kazamin fada a Lebanon wanda ya halaka mutane 47, yayin da Isra'ila ta tabbatar da mutuwar sojojinta hudu, lamarin da ya kara janyo tarnaki ga kokarin shugaban Amurka Donald Trump, na cimma sulhu da Iran, domin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.