1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta halaka masu karbar kayan agaji a Gaza

February 29, 2024

Wani asibiti da ke Gaza ya ba da rahoton mutuwar akalla Falasdinawa 50 yayin da dakarun Isra'ila suka bude musu wuta a lokacin da suke tururruwar karbar kayan agaji a Kudancin yankin da ya fara fama da barazanar yunwa.

https://p.dw.com/p/4d1dV
Nahostkonflikt | Al-Aqsa Martyrs Krankenhaus in Dair El-Balah
Hoto: Ali Hamad/APA Images via ZUMA Pres/picture alliance

Daraktan asibitin na Al-Chifa ya ce galibin wadanda sojojin na Isra'ila suka kashe mata ne da yara kanana, sannan kuma ya kara da cewa an samu mutane akalla 120 da suka jikkata sakamakon wannan al'amari da ya auku a birnin Naplouse, birni mafi girma da ke Kudancin Gaza.

To sai dai ma'aikatar kula da lafiya ta Hamas ta ce adadin wadanda suka mutu ya haura mutum 70 sannan wadanda suka jikkata sun kai mutum 280 inji kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP.

Daga nasu bangare dakarun Isra'ila sun ki su ce uffan kan wannan lamarin da kawo yanzu rayukan da suka salwanta ke ci gaba da karuwa.