1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta ce ta dakatar da kai hare-hare a Gaza

October 20, 2025

Hukumomin Isra'ila, sun ce sun dakatar da hare-hare a Gaza. Da farko dai rundunar sojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta yi barin wuta a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, bayan da dakarunta suka fuskanci hari.

https://p.dw.com/p/52G3J
Motocin soji na Isra’ila a kan iyakar Zirin Gaza
Motocin soji na Isra’ila a kan iyakar Zirin GazaHoto: Amir Cohen/REUTERS

Isra'ila ta sanar da dakatar da hare-haren jiragen sama a Zirin Gaza, hare-haren da a cewar hukumomin lafiya na yankin Falasdinu, suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 45.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai hari kan wasu wurare da ke karkashin ikon Hamas ne, bayan mayakan kungiyar sun kai wa dakarunta hari a yankin Rafah da ke kudancin Gazar, inda suka kashe sojoji biyu.

Sai dai kungiyar Hamas ta ce Isra'ila na neman hujja ne kawai don sake ta da fada.

Bangarorin biyu dai na zargin juna da karya yarjejeniyar tsagaita wutar da Shugaban Amurka Donald Trump ya taimaka wajen kulla ta, wadda ta dauki kwanaki tara kacal kafin sake hare-hare.