1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta ce bisa kuskure ta kashe jami'an agaji a Gaza

April 2, 2024

Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana kisan da dakarun kasar suka yiwa ma'akatan bada agajin jinkai bakwai na 'World Central Kitchen' a matsayin kurkure da basu taba tunanin hakan za ta kasance ba.

https://p.dw.com/p/4eM4u
Motar jami'an agajin jinkai na World Central Kitchen da sojojin Isra'ila suka kashe a Gaza.
Motar jami'an agajin jinkai na World Central Kitchen da sojojin Isra'ila suka kashe a Gaza.Hoto: Ali Jadallah/Anadolu/picture alliance

Firaiministan ya ce lokaci ne na yaki da komai zai iya faruwa. Kazalika suna ci gaba da duba na tsanaki kan lamarin tare da tattaunawa da gwamnatocin kasashen da lamarin ya shafa na mutuwar 'yan asalin kasashensu a zirin Gaza.

karin bayani: Harin Isra'ila ya kashe jami'an agaji 7 'yan kasar waje a Gaza

A wani jawabi da ya gabatar ta kafar talabijin Netanyahu ya bayyana cewa za su tabbatar da cewa an kare afkuwar hakan a nan gaba.