1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila ta amince da murabus din Aharon Haliva

April 22, 2024

Shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar sojin Isra'ila Janaral Aharon Haliva ya yi murabus, bayan amincewa da gazawarsa a harin ba-zata da Hamas ta kaddamar kan Isra'ila a ranar bakwai ga watan Oktobar 2023.

https://p.dw.com/p/4f4Jy
Aharon Haliva
Aharon HalivaHoto: Israel Defense Forces via AP/picture alliance

Rundunar sojin kasar ce ta bayyana haka yau Litinin, a daidai lokacin da Isra'ilar ke ci gaba da ruwan wuta a yankin Zirin Gaza da ta yi wa raga-raga.

Janaral Haliva shi ne jami'in sojin Isra'ila na farko da ya sauka daga mukaminsa saboda gaza kare afkuwar harin na Hamas, wanda ya ballo yaki a Gaza tare da janyo bincike mai zurfi kan sojoji da gwamnatin Tel Aviv.

Har'ila yau isra'ila ta yi suka ga rahoton da ke cewa babbar kawarta Amurka na duba yiwuwar sanya takunkumi kan wasu sojojinta na rundunar IDF, sakamakon zargin da ake musu da take hakkin dan Adam a yakin da take yi a Gaza.