1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila: Netanyahu na fuskantar bore daga majalisar yaki

May 19, 2024

Guda daga cikin mambobin majalisar yaki ta Isra'ila, Benny Gantz ya yi barazanar yin murabus idan ba a kawo karshen Hamas ba.

https://p.dw.com/p/4g2SC
Firanministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firanministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Hoto: Menahem Kahana/AFP

Guda daga cikin mambobin majalisar yaki ta Isra'ila, Benny Gantz ya ce, ya na son majalisar ta samar da wasu tsare-tsare guda shida kan yakin da kasar ke yi da kungiyar Hamas nan da ranar 6 ga watan Junin 2024.

Gantz wanda ya yi barazanar yin murabus idan har Firanministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bai amince da bukatar shi ba, na son ganin an cimma muradun ne da suka hada da kawo karshen kungiyar Hamas a Gaza da tabbatar da tsaron Isra'ila ga yankin Falasdinu da kuma ceto 'yan Isra'ila da ake tsare da su.

Sai dai kuma Mista Netanyahu ya yi watsi da wa'adin da Gantz ya bayar, inda ya ce kalaman nasa ka iya sa a yi nasara kan Isra'ilar. Tun bayan fara yakin Gaza ne dai Gantz ya shiga majalisar yakin a matsayin alama ta hadin kan kasa.