Isra´ila na shirin kutsawa cikin Libanon | Labarai | DW | 22.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra´ila na shirin kutsawa cikin Libanon

Isra´ila ta hada kawunan dubban sojojinta na wucin gadi akan iyakarta da Libanon, abin da ke kara fargabar cewa tana shirin kaddamar wani mamaye ta kasa. To amma wata majiyar soji ko da yake ba ta kawad da yiwuwar kutsen ba, ta ce za´a girke sojoji dubu 3 don karfafa kai hare hare na tsallaken iyaka da nufin lalata sansanonin kungiyar Hisbollah. A kuma halin da ake ciki babban sakataren MDD Kofi Annan yayi gargadin cewa duk wani mamayen da isra´ila zata yiwa Libanon zai janyo munanan hare hare daga bangaren Hisbollah. Tun da farko kuwa ministan tsaron Libanon Elias Al-Murr ya ce a shirye sojojinsa suke su shiga filin daga idan isra´ila ta mamaye kasar. Shi ma shugaban kasa Emile Lahoud ya furta haka a wata hira da tashar telebijin ta CNN. Bayan an shafe kwanaki 10 ana batakashi, mutane kimanin 340 aka kashe a Libanon yayin da sama da 30 suka rasa rayukansu a bangaren Isra´ila kana kuma kusan rabin miliyan sun tsere daga Libanon.