Isra′ila: Majalisa ta amince da sabon kawance | Labarai | DW | 13.06.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila: Majalisa ta amince da sabon kawance

Majalisar dokokin a Isra'ila ta Knesset ta kawo karshen mulkin firaminista Benjamin Netanyahu na kusan shekaru goma sha biyu bayan amincewa da kawancen hadaka na jam'iyu takwas.

'Yan majalisar dokokin Israila ta Knesset sun kada kuri'ar zaben sabon firaministan kasar, a wani kawance na jam'iyyu takwas da ya kawar da firaminista Benjamin Netanyahu daga karagar mulki a karon farko cikin kusan shekaru goma sha biyu.

Gamayyar jam'iyun adawa guda takwas masu karamin rinjaye da kujeru 61 cikin 120 a majalisar ne, suka mayar da jam'iyar shugaba Natanyahu ta adawa. 

Bayan da yan adawar suka samu yadda suke so, sun maye gurbin Natayanhun da Naftali Bennett mai sassafcin ra'ayi a matsayin sabon firaministan na Isra'ilar.