1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa sabuwar rundunar tsaro na ta da kura a Isra'ila

Mahmud Yaya Azare AMA
April 3, 2023

Majalisar ministocin Isra'ila ta amince da kafa sabuwar rundunar da za ta tunkari matsalolin tsaro da ke hana zaman lafiya tsakanin kasar da yankin Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/4PeRv
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanjahu
Firaministan Isra'ila Benjamin NetanjahuHoto: Ohad Zwigenberg/AP Photo/picture alliance

Bayan kwashe kwanaki suna mahawara, daga karshe majalisar ministocin Isra'ila karkashin jagorancin Firaminista Benjamin Netanyahu, ta laminta da zaftare kasafin kudin wasu ma'aikatun gwamnati don kafa sabuwar rundunar tsaron kasa da za ta kasance karkashin jagorancin ministan tsaron al'umma Itamar Ben-Gvir wanda a baya yayi barazanar murabus daga aikinsa, muddin ba a lamunce masa kafa rundunar ba.

Karin Bayani: Dambaruwar siyasa na kara kamari a Isra'ila

Duk da cewa Itamar Ben-Gvir ya ce, za'a kafa wannann rundunar ce don tunkarar ta'adancin Falalsdinawa da ba wa Yahudawa 'yan kama wuri zauna tsaro na musamman, da dama daga cikin ma'aikatun gwamnati na yi wa rundunar kallon tamkar kirkirar kishaya ce ga jami'an tsaron gwamnati.

Babban jami'in 'yan sandan Isra'ila, Yohanan Danino, yace ba zai lamunta da yin aiki tare da wannan sabuwar rundunar ba wacca ya siffanta da yan bangar siyasar siyasanci da ke kokarin kishiyantar aikin yan sanda, baya ga wasu 'yan sandan da suka suka shirya jerin gwanon nuna adawa da kafa wannan sabuwar runduna.

Karin Bayani: Dakatar da sake fasalin shari'a a Isra'ila

Shugabar hukumar kare hakkin bil'Adama ta Majalisar Dunkiya Duniya a kasar ta Isra'ila, Francisca Albanese cewa ta yi da "Ganin yadda batanci a Falasdinawa ke kara munana a Isra'ila, daukar mutanen gari a matsayin masu ayyukan sa kai na tsaro karkashin jami'an gwamnati abu ne mai matukar hatsari da zai sanya masu zaluntar Falalsdinawa samun kafar tsira daga hukunci."

Tuni dai hukumar Falalsdinawa ta yi fatali da matakin kafa rundunar.