1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaminista Benjamin Netanyahu na fuskantar sabon kalubale

Zulaiha Abubakar MNA
December 26, 2019

A wannan Alhamis ake gudanar da zaben shugabancin jam'iyyar Likud mai mulki a Isra'ila, inda ake fafatawa tsakanin Firaminista Benjamin Netanyahu mai shekaru 70 da jagoran hamayya Gideon Saar.

https://p.dw.com/p/3VL0p
Israel: Rakete zwingt Benjamin Netanyahu / Netanjahu  in Bunker
Hoto: picture-alliance/AP/G. Tibbon

Wanda ya yi nasara a zaben shugabancin jam'iyyar ta Likud dai, zai jagoranci jam'iyyar a zaben da kasar za ta gudanar a karo na uku nan gaba. 'Yan takarar dai sun shafe makwanni suna yawon neman goyon bayan 'yan jam'iyyar a fadin kasar.

Ko da yake Gideon Saar ya aikewa da Netanyahu bukatar gudanar da muhawara a bayyanar jama'a tun da farko, amma Netanyahun ya ki amincewa.

Tuni an bude cibiyoyin zaben da yawansu ya kai 100 domin kada kuri'un sabon shugaban jam'iyyar ta Likud.

Magoya bayan Firaminista Benjamin Netanyahu na fargabar rashin nasara a zaben shugabancin jam'iyyar.