Isra′ila: An nemi gurfanar da Netanyahu kan rashawa | Labarai | DW | 14.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Isra'ila: An nemi gurfanar da Netanyahu kan rashawa

'Yan sandan Isra'ila sun nemi a gurfanar da Firaminista Benjamin Netanyahu a gaban shari'a saboda laifuka na cin hanci da rashawa da kuma zamba cikin aminci.

Wannan na zuwa ne bayan 'yan shekaru ana binciken zargin da ake wa Firaiministan na amsar rashawa daga wasu abokansa yayin da shi kuma ke basu ayyuka na musanman, akwai kuma zargin da jami'an tsaron suka yi masa kan yin katsalandan a harkokin wasu kafaffen yada labarai da ya fifita fiye da saura.

Tuni dai Firaminista Netanyahu ya musanta wadannan zarge-zargen da ya ce yunkuri ne na ganin an tilasta masa sauka daga karagar mulki, a cewarsa wannan ba shi bane karon farko da ake kira na a tuhume shi kan laifukan da bai aikata ba. Yanzu dai ana sa ran mika koken 'yan sandan gaban lauyan gwamnati, a yayin da jam'iyyun adawa a daya bangaren suka bukaci Netanyahu da ya yi murabus daga mukaminsa.